Gwamnatin Najeriya ta Haramta Shigowa da Kayayyaki Guda 25 Cikin Kasar:

Gwamnatin Najeriya ta Haramta Shigowa da Kayayyaki Guda 25 Cikin Kasar:

A kalla Gwamnatin Najeriya ta Haramta Shigowa da Kayayyaki Guda 25 Cikin Kasar: Shugaban Kwastom Hamid Ali.

A irin Yunkurin da Gwamnatin Najeriya take yi  na bunkasa sana'o'i da masana'antun cikin gida samarwa da matasa aikin yi, Gwamnatin Tarayya ta sake haramta shigo da wasu kayayyaki guda 25 daga kasashen ketare. Kayayyakin  kamar yadda Ma'aikatar Kudi ta Tarayya ta sanar, sun hada da;

.

1. Tsuntsaye masu rai ko marasa rai,

2. Naman Alade ko na Shanu.

3. Kwai ko da kuwa na kyankyasa ne.

4. Man girki.

5. Rake ko wani nau'in sukari.

6. Kakiden Koko (Cocoa Butter).

7. Taliya.

8. Kayan sha na 'ya'yan itatuwa.

9. Ruwan sha kowanne iri da sinadaran k'arin kuzari.

10. Sumunti.

11. Magunguna da suka hada da paracetamol da sauransu.

12. Tarkacen magunguna marasa amfani.

13. Sabulai da garin wanki.

14. Maganin sauro.

15. Kayayyakin amfanin tsaftace jikin mata ko na yara.

16. Tsofaffin tayoyi.

17. Dukkan kayayyakin da ake yin su da takarda.

18. Katin waya.

19. Kafet ko dardumar daki.

20. Takalma, jakunkunan hannu da na kaya.

21. Kwalabe.

22. Tsofaffin firji da na'urar sanyaya daki.

23. Tsofaffin motocin da suka wuce shekaru 15 da k'erawa.

24. Kayan kawa na katako.

25. Biro na rubutu.


Jama'a ko Yaya kuke Kallon Irin wannan Cigaba da Gwamnatin Najeriya ta Samu?


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky