Gwamnatin Masar Zata Hukunta Mutanen Da Suka Ki Gudanar Da Zabuka A Kasar

Gwamnatin Masar Zata Hukunta Mutanen Da Suka Ki Gudanar Da Zabuka A Kasar

Kwamitin kula da zabuka a kasar Masar ya sanar da cewa: Suna ci gaba da tantance sunayen mutanen da suka ki kada kuri'a a zaben shugaban kasa da aka gudanar a Masar da nufin mika su ga ma'aikatar shari'ar kasar.

Shugaban kwamitin kula da zabuka a kasar Masar Lasheen Ibrahim a jiya Litinin ya fitar da sanarwar cewa: Bayan kammala tantance sunayen mutanen da suka ki kada kuri'a a zaben shugaban kasa da aka gudanar a Masar, kwamitinsa zata mika sunayen ga ma'aikatar shari'ar kasar domin zartar da irin hukuncin da ya dace kansu.

Ibrahim ya kara da cewa: Kwamitinsa bata da hakkin cewa ga irin hukuncin da ya dace da mutanen da suka ki gudanar da zabuka a kasar, aikinta kawai tantance sunayen mutane tare da mika su ga ma'aikatar shari'ar Masar, kuma ga dukkan alamu aikin zai dauki lokaci mai tsayi saboda mutanen da suka ki yin zaben sun kai miliyoyi.

Kididdiga ta fayyace cewa mutane kimanin 34,823,986 ne suka ki kada kuri'unsu a zaben shugaban kasa da aka gudanar a Masar a watan Maris na wannan shekara da aka shelanta Abdul-Fatah Al-Sisi a matsayin wanda ya lashe zaben. 


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky