George Weah ya Lashe Zabin Shugaban Kasar Liberia

George Weah ya Lashe Zabin Shugaban Kasar   Liberia

Hukumar zaben Liberia ta sanar a jiya Alkhamis cewa Tsohon shahararren dan kwallon kafa George Weah ya lashe zaben shugaban kasar zagaye na biyu da kashi 61,5.

A cikin wata sanarwa da ta fitar , hukumar zaben kasar Liberia ta tabbatar da cewa Tsohon shahararren dan kwallon kafa ne na Duniya wato George Weah shi ne ya lashe zaben shugaban kasar da kashi 61,5% na kuri'un da aka kada yayin da abokin hamayarsa mataimakin shugaban kasa mai ci mista Joseph Boakai ya samu kashi 28,8.

Jim kadan bayan samun labarin nasarar ta Mista Weah, magoya bayansa suka fara bukukuwan nuna murnarsu a babban birnin kasar na Monrovia.

A ranar 22 ga watan janairu na shekara mai kamawa ne ake sa ran za a rantsar da sabon shugaban kasar ta Liberia.

A yayin yakin neman zabe, Mista George Weah ya yi alkawarin farfado da tattalin arzikin kasar ta hanyar yaki da barnar dukiyar kasa


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Arba'een
mourning-of-imam-hussain
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky