Faransa Za Ta Gina Gidajen Wake-wake A Saudiyya

Faransa Za Ta Gina Gidajen Wake-wake  A Saudiyya

Faransa za ta taimaka wa kasar Saudiyya wajen samar da katafaren dakin wassani da wake wake, yayin da za'a fara haske fina finan Saudiyya a wajen bikin baje kolin fina- finai na ''CANE''.

Wannan bayyanin dai ya fito ne a yayin ziyarar da matashin yarima mai jiran gado na Saudiyyar ke yi a kasar ta Faransa.

Hakan dai na daga cikin manufofin da Mohamed Ben Salman, ya sanya a gaba na kakkabe kasar ta Saudiyya mai ra'ayin addinin Islama na wahabiyanci, ta hanyar bullo da harkokin da suka shafi al'adu da walwalar al'umma.

Ministan al'adu na Saudiyya, Awad Al'awad ya bayyana yarjeniyoyin da masu matukar mahimmanci.

A wani labari kuma a ranar 18 ga wannan wata na Afrilu ne aka tsara Saudiyyar bude kofar gidan sinimarta na farko a babban birnin kasar Riyadh, wanda kuma shi ne share fagen bude wadansu gidajen sinimar kusan 100 a fadin kasar nan da shekarar 2030.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky