Faransa Da Amurka Sun Tattauna A Kan Iran

Faransa Da Amurka Sun Tattauna A Kan Iran

shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya tattauna ta wayan tarho da takwaransa na kasar Amurka Donald Trump inda ya bayyana masa muhimmancin ci gaba da mutunta yerjejeniyar nukliya tsakanin Iran da Kasashe 5+1

Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya nakalto wani bayani wanda Fadar Elize ta fitar a jiya Alhamis wanda yake cewa shugaban Macron ya bayyanawa Trump muhimmancin aiwatar da yarjejeniyar kamar yadda take. 

Wannan tattaunawar ta Macron da Trump ta zo ne a dai-dai lokacinda shugaban Amurkan zai dauki matsayi a kan ci gaba da aiki da yerjejeniyar, ko yin watsi da ita a yau Jumma'a. A ranar 13 ga watan Octoban da ya gabata dai shugaban ya bayyana cewa Iran tana sabawa yerjejeniyar duk tare da cewa hukumar IAEA ta tabbatar da akasin haka har sau 8.

A lokacin ne Trump ya aikawa majalisar dokokin kasar batun yarjejeniyar don ta dauki matsayi a kanra cikin kwanaki 60, sai dai majalisar bata yi komai ba har  aka maida masa da takardun.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky