Dalibai sun yi kira da gwamnati ta saki Sheikh Ibrahim Zakzaky

Dalibai sun yi kira da gwamnati ta saki Sheikh Ibrahim Zakzaky

A jiya laraba 30 ga watan Agustus 2017 ne,wasu dalibai karkashin damdamalin daliban Harkar Musulunci a Nigeriya suka gudanar da muzaharar neman a saki Sheikh Zakzaky a garin Abuja.
Sheikh Zakzaky ya kwashe fiye da shekara daya da rabi yana tsare tun bayan harin da sojoji suka kai masa a gidansa dake Gyellesu.
Masu muzaharar sun fara ta ne daga kasuwar Wuse,kana suka tsallaka begger suna wakokin dake ishara ga neman gwamnati ta saki shehin malamin.
A Kaduna ma anyi irin wannan muzaharar ta neman a saki Shehin malamin amma 'yan sanda sun yi kokari su kawowa mata cikas ta hanyar antaya wa masu muzaharan barkonon tsohuwa amma duk da haka an kammala ta lafiya.
In ba a manta ba,a disambar 2016 wata babbar kotu a Abuja tayi hukunci da saki Sheikh Zakzaky da mai dakinsa tare da biyansu diyya amma gwamnati tayi biris da wannan umurnin kotun.
Ko menene dalili?

Abuja

Abuja

Abuja

Abuja


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Quds cartoon 2018
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2017)
پیام امام خامنه ای به مسلمانان جهان به مناسبت حج 2016
We are All Zakzaky