DALIBAI SUN YI KIRA DA A SAKI SHEIKH IBRAHIM ZAKZAKY A GARIN ABUJA NIGERIYA

DALIBAI SUN YI KIRA DA A SAKI SHEIKH IBRAHIM ZAKZAKY A GARIN ABUJA NIGERIYA

A jiya laraba ne,daliban manyan makarantu na harkar musulunci suka gudanar da muzaharar lumana a garin Abuja domin kira da gwamnatin Nigeriya da ta bi umurnin kotu ta sakin Sheikh Zakzaky da mai dakinsa Malama Zeenat wa’yanda suka kasance a tsare tun bayan lokacin da sojojin Nigeriya suka afka ma Sheikh da almajiransa a watan Disambar 2015.
Shugaban kungiyar ta daliban,S I Ahmad a wata takarda da suka rabawa manema labarai wadda suka yi ma take da “Lokaci yayi da gwamnatin Nigeriya zata saki Sheikh Zakzaky” ya bayyana cewa:
“Mai yasa hukumomin Nigeriya suka ki su bi umurnin babban kotu,su saki Jagoran harkan musulunci a Nigeriya,Sheikh Zakazaky tare da mai dakinsa wa’yanda suke tsare ba akan ka’ida ba?
“Yanzu ta bayyana ma duniya cewa Sheikh Zakzaky da mai dakinsa Malama Zeenah,suna tsare fiye da shekara daya da rabi ba tare da wata tuhuma ko laifi ba tun bayan farmakin rashin imani da sojojin Nigeriya suka kai ma malamin da almajiransa wanda yayi sanadiyyan asaran rayukan daruruwan almajiransa maza da mata da kananan yara a Zariya.Sojojin Nigeriya sun afka ma Sheikh Zakzaky da matansa a gidansa.Sun harbi malamin a wajaje masu yawa a jikinsa tare matansa,suka kashe masa ‘ya’ya a gabansa.
Daliban masu muzaharan lumana din sun kasance cikin tsari sanye da riguna iri wa’yanda aka rubuta a saki Zakzaky da huluna,suna rike da banoni wa’yanda aka rubuta a saki Zakzaky da kuma gwamnati tabi umurnin kotu,suna wakoki na kira da a saki Zakzaky.An kammala muzaharan lafiya ba tare da wani matsala ba

Abuja

Abuja

Abuja

Abuja

Abuja

Abuja


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky