Dakarun Iraki Suna Ci Gaba Da Fatattakar 'Yan Ta'addan ISIS A Mausul

Dakarun Iraki Suna Ci Gaba Da Fatattakar 'Yan Ta'addan ISIS A Mausul

Dakarun gwamnatin Iraki da sauran dakarun sa kai na al'ummar kasar suna ci gaba da fatattakar 'yan ta'addan ISIS (Daesh) a yammacin birnin Mausul.

Tashar talabijin ta al'alam ta bayar da rahoton cewa, a ci gaba da kaddamar da faraki da dakarun Iraki ke yi domin kwace iko da birnin mausul daga hannun 'yan ta'addan takfiriyyah na ISIS, a jiya dakarun na Iraki sun gano wani wuri da 'yan ta'addan suke hada bama-bamai da nakiyoyi, kwanaki biyu bayan gano wasu sanadarai na hada makamai masu masu guba, da suka kai kimanin ton 100.

Rahoton ya ce dakarun na Iraki sun kammala tsarkake yankunan gabashi da kudancin Mausul baki daya daga 'yan ta'addan wahabiyyah takfiriyyah na ISIS, yayin da sauran yankunan kuma ake ci gaba da fafatawa.

A makon da ya gabata ne dakarun Irakin suka hangi wani babban jirgin sojin Amurka yana safke wasu akwatuka da ake sa ran makamai nea  cikinsu, a yankin da ke karkashin ikon ISIS a yammacin Mausul.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Quds cartoon 2018
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2017)
پیام امام خامنه ای به مسلمانان جهان به مناسبت حج 2016
We are All Zakzaky