Da'ish Ta Sace Mutane A Siriya

Da'ish Ta Sace Mutane A Siriya

Bayanai dag Siriya na cewa kungiyar 'yan ta'adda ta (IS) ta sace mata da yara a kalla 36 bayan mummunan harin data kai a makon da ya gabata a lardin Suweda.

Kungiyar dake sa ido kan al'amuran kare hakkin bil adama ta OSDH a Siriyar, ta sanar da cewa mata da yaran 'yan kabilar Druze an yi garkuwa dasu ne a yayin farmakin da kungiyar mayakan dake ikirari da sunan jihadi ta IS ta kai a lardin a ranar 25 ga watan Yulin nan, inda mutane sama da 250 suka rasa rayukansu.

Wadanda akayi garkuwa da su sun hada da mata 20 da kuma yara 16 a cewar kungiyar ta OSDH da kuma wani shafin intaner Sueda24.

Kungiyar dai ta IS bata fitar da wani bayyani ba kan wanann labarin.

Harin da kungiyar ta IS ta dauki alhakin kai wa a lardin na Sueda a baya bayan nan, shi ne irinsa mafi muni, tun bayan da kasar ta Siriya ta tsuduma cikin yaki a shekara 2011.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky