Cibiyar Ahlul-Baiti{a.s} Ta Duniya Tayi Allah Wadai Da Kisan Kiyashin Da A Ke Ma Musulmi A Myanmar

Cibiyar Ahlul-Baiti{a.s} Ta Duniya Tayi Allah Wadai Da Kisan Kiyashin Da A Ke Ma Musulmi A Myanmar

Cibiyar Ahlul-Baiti{a.s} ta duniya tayi tofin Allah wadai da kisan kiyashin da a ke ma musulumi a kasar Myanmar ta kuma yi kira ga kasashen duniya da su tsoma baki.

Kamfanin dillanci labarai na Ahlul-Baiti{a.s}-abna-cibiyar Ahlul-Baiti ta fitar da bayani akan kisan kiyashin da ake ma al’ummar musulmi a Myanmar sannan kuma tayi kira ga kasashen duniya da su tsoma baki cikin lamari,

Al’ummar rohingya wadanda aka jima a na zalunta da sunan cewa su ba ‘yan kasa bane, cibiyar Ahlul-Baiti{a.s} a cikin bayanin ta tayi ishara da yadda ‘yan buda masu tsatsauran ra’ayi da hadin kan sojoji da kuma goyon bayan hukuma suka aukama musulmi da kisa da kuma kone gidaje,masallatai,da kuma shaguna inda wasu kuma aka rabasu da gidajen su.

Bayanin kuma ya yi nuni da rawar da wahabiyawa masu kafirta mutane suka taka a cikin rura wutar rikicin Myanmar ta fuskar nuna rashin Imani ga duk wani wanda ba su ba musulmi ne ko buda ko kirista ya tai maka wajen tunzura yan buda da sunan fada tsakanin musulmi da buda.

Ya zuwa yanzu sama da mutane 400 ne suka rasa yawukan su a cikin sati guda, a tsawon shekara 5 kuma daruruwan mutane ne aka kashe ko kuma suka salwanta a cikin ruwa yayin da suke gudun hijira a halin yanzu miliyoyin mutane ne suka bar gidajen su.

Cibiyar Ahlul-Baiti{a.s} ta duniya wadda ke da wakilai a fadin kasashe da dama tana kira ga al’umma zuwa ga wadannan abubuwan kamar haka.

1-hakikani addini shine kadaita Allah, tarbiya,son juna, zaman tare. Saboda haka duk addini ko hukumar da take kashe al’umma da sunan addini su sani sun saba hanya.

2-kungiyoyin kasa da kasa suna kira ga kare hakin ko wane dan kasa a duk inda yake.

3-wata hukuma bata da hakin kisa,Konawa,ko kuma kurara mutun saboda shi ba dan kasa ba ne.

4-a halin da kasashen duniya ke karbar yan gudun hijiya amma sai ga shi Myanmar na korar mutanen da suka rayu tsawon zamani da sunan bay an Myanmar ba ne.

5-rawar da wahabiyawa suke takawa wajen gogama addini musulunci kashin kaji ta hanyar nuna kiyarya ga kowa ne mutun wannan ne ya kara bay an buda masu tsatsauran ra’ayi damar aukama musulmi da sunan fada tsakanin musulmi da buda.

6-kasar Amurka da yan kanzaginta sunyi  shiru suna kallon ana kasha musulmi tsawon shekaru basu ce huffan ba amma da zarar wani musulmi ya aikata ba dai dai ba yanzu kaji su cika duniya da surutai.

7-muna kira ga kungiyar hadin kan musulmin duniya da kuma kasashen musulmi da su tashi tsaye domin hana hukumar Myanmar ci gaba da kisan kiyashin da ake ma musulmi.kamar yadda sayyid khamna’I ya fada a cikin sakon hajji cewa; kare al’umma yan tsiraru na kasar Myanmar ya doru ne kan shuwagabannin kasashen musulmi .

8-a kuma gargadi kasar Myanmar akan abunda take aikatawa sannan a kira zaman sulhu tsakanin wadanda abun ya shafa da warware abun ta hanyar dokokin kasa da kasa.

9-muna kira ga yan gwagwarmaya da musulmin duniya da su nuna kin amincewar su ga abunda ke faruwa ta hanyar kiraye-kiraye da sauti da ban da ban. Domin farkar da duniya illar kisan kiyashi.

الَّذينَ أُخرِجوا مِن دِيارِهِم بِغَيرِ حَقٍّ إِلّا أَن يَقولوا رَبُّنَا الله وَلَولا دَفعُ الله النّاسَ بَعضَهُم بِبَعضٍ لَهُدِّمَت صَوامِعُ وَبِيَعٌ وَصَلَواتٌ وَمَساجِدُ يُذكَرُ فيهَا اسمُ اللَّهِ كَثيرًا وَلَيَنصُرَنَّ الله مَن يَنصُرُهُ إِنَّ الله لَقَوِيٌّ عَزيز. ﴿سوره حج، آیه ۴۰﴾

مجمع جهانی اهل‌بیت(ع)

 


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Quds cartoon 2018
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2017)
پیام امام خامنه ای به مسلمانان جهان به مناسبت حج 2016
We are All Zakzaky