Bullar Sabon Rikici A Gaza Ya Tada Hankalin Duniya

Bullar Sabon Rikici A Gaza  Ya Tada Hankalin Duniya

Majalisar dinkin duniya ta yi kira da a kai zuciya nesa don hana kara tsananta yanayin da ake ciki a zirin gaza.

Mai shiga tsakani na musamman a shirin wanzar da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya na MDD Mista Nickolay Mladenov ya yi kira ga bangarorin daban-daban na Palasdinu da Israi'la su zauna da su yi hakuri da juna don hana kara tsananta hali da ake ciki a tsakaninsu.

Ya kara da cewa, kamata ya yi bangarorin daban-daban masu ruwa da tsaki na Palasdinawa da 'yan Isra'ila, da su yi hakuri don kaucewa hasarar rayuka.

Rahotannin dai sun nuna cewa sojojin mamaya na Isra'ila na ci gaba da kai hare-hare a zirin na Gaza har zuwa yau Laraba, bayan ruwan rokokin da aka kai zuwa Israi'lar.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky