Buhari Ya Soke Wata Kwangilar Sayen Makamai Daga 'Isra'ila' Ta Dala Miliyan 195

Buhari Ya Soke Wata Kwangilar Sayen Makamai Daga 'Isra'ila' Ta Dala Miliyan 195

Shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya ya soke wata kwangilar sayen makamai daga haramtacciyar kasar Isra'ila da ta kai dalar Amurka miliya 195 saboda alamun rashin gaskiya da ya shigo cikin cinikin.

Rahotanni sun ce shugaba Buharin ya ba da umurnin soke kwangilar ce bayan da ya gano wasu alamu na rashin gaskiya cikin yadda aka gudanar da kwangilar sayen makaman tsakanin wasu jami'an gwamnatin Nijeriya da na haramtacciyar kasar Isra'ilan.

Rahotannin sun ce a cikin umurnin da shugaba Buharin ya ba wa ministan shari'a kuma alkalin alkalai na Nijeriyan Abubakar Malami, ya bukaci da a soke kwangilar kamar yadda kuma ya bukaci babban mai ba wa shugaban kasa shawarar kan harkokin tsaro da kuma babban daraktan Hukumar tsaro ta kasar NIA da su gudanar da bincike don gano yadda aka yi har aka kulla kwangilar, kamar yadda kuma ya bukaci da a tilasta wa kamfanin na 'Isra'ila' da ya biya dala miliyan 50 da ya karba na soman tabin kwangilar.

A bisa wannan kwangilar wacce aka kulla ta a shekarar bara 2017 da aka ce akwai hannun ministan sufuri, Rotimi Amaechi, a ciki za a sayo wasu jirage masu saukar ungulu na musamman da wasu makamai da kayayyakin aiki soji ga sojojin ruwan Nijeriya din ne, to sai dai kuma sakamakon wani bincike da aka gudanar an gano sha'anin rashin gaskiya cikin cinikin lamarin da ya sanya shugaba Buhari soke kwangilar da kuma gudanar da bincike kanta.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky