Buhari Ya Sauya Ranar Dimokradiyya A Nijeriya Zuwa Ranar 12 Ga Watan Yuni

Buhari Ya Sauya Ranar Dimokradiyya A Nijeriya Zuwa Ranar 12 Ga Watan Yuni

Shugaban Muhamadu Buhari na Nijeriya ya sauya ranar dimokaradiyyar kasar daga 29 ga watan Mayu na kowace shekara zuwa ranar 12 ga watan Yuni don girmama zaben 12 ga watan Yunin shekarar 1993 da aka sanar da Cif Moshood Abiola a matsayin wanda ya lashe shi.

Shugaba Buhari ya sanar da hakan ne cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar dauke da  sanya wa hannun shugaban inda bayan sanar da ranar 12 ga watan Yunin a matsayin ranar dimokradiyyar har ila yau kuma ya ce za a karrama Cif Moshood Abiola wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a  ranar 12 ga watan Yuni na 1993 da lambar girmamawa mafi daraja a kasar  wato GCFR.

Har ila yau kuma shugaba Buhari ya ce za'a  karrama  Alhaji Babagana Kingibe wanda suka yi takara da Cif Abiola din da lambar girma ta biyu a kasar wato GCON kamar yadda zai ba wa marigayi Cif Gani Fawehimi, fitaccen mai kare hakkokin bil'adama na kasar da irin wannan lambar girmar.

A baya dai ana gudanar da ranar dimokradiyya din a Nijeriya ne a ranar 29 ga watan Mayu don tunawa da ranar da sojoji suka mika mulki ga fararen hula a shekarar 1999, to sai dai shugaba Buharin ya ce ranar 12 ga watan Yuni din ta fi wancan ranar muhimmanci don kuwa a ranar ce aka gudanar da mafi tsaftan zabe a kasar amma gwamnatin mulkin soji ta Janar Babangida ta soke zaben.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky