Buhari Ya Kaddamar Da Kwamitin Kula Da Tasirin Budaddiyar Kasuwa A Afrika

Buhari Ya Kaddamar Da Kwamitin Kula Da Tasirin Budaddiyar Kasuwa A Afrika

Shugaba Muhammadu Buhari na tarayyar Najeriya ya kaddamar da kwamiti mai kula da amfanin da yan kasa zasu samu a budaddiyar kasuwa a nahiyar Afrika

Kamfanin dillancin labaran NAN na Najeriya ya ce shugaban ya kaddamar da kwamitin ne jiya Litinin a fadar shugaban kasa, sannan ya bayyana cewa daga yanzu gwamnatinsa ba zata sake sanya hannu  a kan wata yerjejeniya ko kongiloli ba sai ta san irin amfanin da yan Najeriya zasu samu sanadiyyarsa.

Kwamitin, wanda ministan masana'antu yake jagoranta yana da shugaban ma'aikata a fadar shugaban kasa a matsayin mataimakin sa. 

Shugaban ya bukaci kwamitin ya tabbatar da cewa ya fitar da matakai na gajeren zango, matsakaici da kuma na dogon zango don magance dukkan matsalolin da zasu iya tasowa kan harkokin kasuwanci a budadiyar kasuwa ta kasashen Afrika. 

Shugaban ya kammala da cewa mahangar Najeriya a harkar kasuwanci tsakanin kasashen Afrika, a matsayinta na kasa ta farko a karfin tattalin arziki a nahiyar, shi ne shigar kayayyakin da aka kera a Najeriya zuwa dukkan kasashen nahiyar.

 


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky