Buhari ya fice zuwa Abidjan domin taron AU-EU

Buhari ya fice zuwa Abidjan domin taron AU-EU

Taron na shugabannin kasahen nahiyar Afirka da Turai zai tattauna ne a kan batutuwa da suka hada da tattalin arziki, da tsaro, da kuma magance matsalar kwararar baki da sauransu.

A ranar Laraba da Alhamis ne ake sa ran shugabannin kasashen za su daddale kan al'amuran da suka fi shafar bangarorin guda biyu.

Ana sa ran shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai tattauna da shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron a gefen taron, inda za su tattauna a kan dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu.

To sai dai gamayyar kungiyoyin fararen hular nahiyar Afirka da ake kira 'Tournons la Page' na kallon taron na Abidjan a matsayin wata haduwa domin kare muradun kasashen Turai kawai.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky