Buhari Ya Dauki Alkawalin Kawo Karshen Tashin Hankula A Cikin Nageria Nan Ba Da Jimawa Ba

Buhari Ya Dauki Alkawalin   Kawo Karshen Tashin Hankula A Cikin Nageria  Nan Ba Da Jimawa Ba

Shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya ya bayyana cewar nan ba da jimawa ba hare-haren da wasu 'yan bindiga da ake cewa makiyaya ne suke kai wa wasu sassa na kasar zai kawo karshe sakamakon irin matakan da gwamnatinsa take dauka.

A wata sanarwa da mai ba wa shugaba Buharin shawara na musamman kan harkokin watsa labarai Femi Adesina ya sanya wa hannu ya ce shugaban na Nijeriya yayi wannan alkawarin ne a yayin da yake ganawa da wasu daraktoci na bangaren tattalin arziki na kasar a fadarsa da ke birnin Abuja inda ya ce bisa la'akari da matakan tsaro da aka dauka musamman a yankunan da wadannan hare-hare suke faruwa lalle nan ba da jimawa ba hare-haren za su zamanto tarihi.

Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa tana sane da irin matsaloli na tsaro da al'umma suke fuskanta sakamakon wadannan hare-hare don haka ya sake jaddada matsayar gwamnatinsa na cika alkawarin da ta yi wa 'yan Nijeriya na tabbatar da tsaron dukiya da lafiyar 'yan kasar, dakatar da cin hanci da rashawa da kuma samar da aikin yi ga matasa.

Cikin 'yan kwanakin baya-bayan nan dai wasu jihohi na Nijeriyan musamman Adamawa, Taraba da Benue sun fuskanci rikice-rikice tsakanin makiyaya da manoma da yayi sanadiyyar mutuwar wani adadi mai yawa na al'ummomin wadannan jihohin.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky