Buhari na da lafiyar sake tsayawa takara a 2019"

Buhari na da lafiyar sake tsayawa takara a 2019

Fadar gwamnatin Najeriya ta ce, shugaba Muhammad Buhari na da koshin lafiyar da zai iya neman sabon wa’adin shugabancin kasa a zaben shekarar 2019.

Mai bai wa shugaban shawara kan kafafen yada labarai, Femi Adeshina ya bayyana haka a yayin zantawa da manema labarai a birnin Abuja.

Adesina ya ce, lafiyar shugaba Buhari ta yanzu ta fi inganci fiye da lafiyarsa ta 2015, lokacin da ya lashe kujerar mulkin kasar.

Adesina ya ce, duk da dai Buhari bai yanke shawarar sake tsayawa takara ba, amma lafiyarsa ba za ta kawo ma sa cikas ba saboda yadda ta inganta tun bayan dawowarsa daga jinya a birnin London.

Adesina ya kuma musanta rade-radin cewa, shugaba Buhari ya nada ministan sufuri, Rotimi Amaechi a matsayin darektan yakin neman zabensa a 2019.

A ranar 7 ga watan Mayun da ya gabata ne, Buhari ya koma London don duba lafiyarsa, yayin da ya dawo gida a ranar 19 ga watan Agustan bara.

Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky