Buhari: Bana Na Cika Azumi Na

Buhari: Bana Na Cika Azumi Na

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ya kammala azumin Ramadan na bana ba tare da ya sha ko daya ba.

Shugaban ya fadi haka ne a yayin da yake ganawa da al'ummar Abuja da suka kai ma sa ziyarar barka da Sallah a fadarsa karkashin jagorancin ministan birnin Tarayya.

A sanarwar da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Femi Adeshina ya fitar, shugaban ya ce: "Ban yi azumin bara ba saboda rashin lafiya, amma a bana na samu cikakkiyar damar yin azumin."

Shugaba Buhari ya shafe watanni yana jinya a Birtaniya a bara, jinyar rashin lafiyar da har ya dawo ba a bayyana ainihin cutar da ke damunsa ba.

Ko a watan Mayun bana, shugaban ya sake komawa Landan domin ganin likitansa bayan ya dawo daga Amurka.

Shugaban wanda ya bayyana aniyar sake neman wa'adin shugabanci na biyu a zaben 2019 ya ce, "ajiye azumi bai wajaba ga musulmin da ke cikin koshin lafiya ba."

Wannan na nufin shugaban ya samu lafiya daga cutar da ya yi fama da ita wacce a baya ta janyo ce-ce-ku-ce a Najeriya inda har wasu suke ganin shugaban ba zai iya shugabancin kasar ba.

A cikin jawabinsa, Buhari ya yi kira ga 'Yan Najeriya su yi aiki don gyara kasar daga matsalolin da ta fada a baya.

"Ba mu da wata kasa da ta wuce Najeriya. Za mu iya hada kai mu ceto ta gaba daya" in ji shi.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky