Boko Haram Ta Kashe Kimanin Mutane 400 A Ckin Watanni 5

Boko Haram Ta Kashe Kimanin Mutane 400 A Ckin Watanni 5

Rahoton kungiyar ta kare hakkin bil'adama ta kasa da kasa, Amnesty International ya ce hare-haren kungiyar 'Boko Haram sun kashe mutane kusan 400 a kasashen Najeriya da Kamaru.

Har ila yau, kungiyar ta kare hakkin bil'adama, ta zargin kungiyar 'yan ta'addar ta Boko Haram,da tafka laifukan yaki ta hanyar bai wa kananan yara maza da mata abubuwa masu fashewa domin kashe mutane masu yawan gaske.

Wani sashe na rahoton kungiyar ya ce; Tun daga 2009 zuwa yanzu kungiyar ta kai hare-haren da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane 20,000 a cikin kasashen Najeriya, Kamaru, da Nijar, sai kuma maida mutane fiye da miliyan biyu da 600,000 zuwa 'yan gudun hijira.

Har yanzu dai kungiyar mai akidar kafirta musulmi tana ci gaba da kai hare-hare a yankin arewa maso gabacin Najeriya da kuma kasashen Kamaru da Jamhuriyar Nijar.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Quds cartoon 2018
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2017)
پیام امام خامنه ای به مسلمانان جهان به مناسبت حج 2016
We are All Zakzaky