Boko Haram Ta Kaddamar Da Wani Mummunan Hari A Kauyen Borno

Boko Haram Ta Kaddamar Da Wani Mummunan Hari A Kauyen Borno

Mayakan kungiyar Boko haram sun kai mumanar hari a kauyukan jihar Borno tare da hallaka mutane da dama.

kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya habarta mayakan  Boko Haram  sun kashe mutane da dama tare da tilasta wa daruruwa tserewa daga gidajensu bayan wani hari da suka kaddamar a karamar hukumar Koduga da ke jihar Bornon Najeriya.

Rahoton ya ce, maharan sun kutsa cikin kauyukan Kofa da Bulabbrin da misalin karfe 7:50 na daren jiya laraba, in da suka yi ta kiran “ Allahu Akbar” a dai dai lokacin da suke barin wuta kan jama’a.

Kazalika mayakan sun kona kauyukan kamar yadda wadanda suka shaida aukuwar lamarin suka tabbatar.

A halin yanzu, daruruwan jama’ar da suka rasa muhallansu sakamakon harin na samun mafaka a Dalori.

Ya zuwa yanzu babu wata sanarwa da ta fito daga gwamnatin Najeriya ko jami'an tsaron kasar.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky