Boko Haram ta kaddamar da kai hari a kan sansanin ‘Yan gudun hijira a Diffa

Boko Haram ta kaddamar da kai hari a kan sansanin ‘Yan gudun hijira a Diffa

Wasu mata biyu ‘yan kunar bakin wake sun tayar da bam a wani sansani da ke garin Kabalewa a jihar Diffa da ke gabashin Jamhuriyyar Nijar inda suka tarwatsa kansu tare da kashe wasu fararen hula biyu a sansanin

Kabalewa, gari ne da ke karbar dubban ‘yan gudun hijirar Boko Haram, kuma mafi yawansu sun fito daga Najeriya.

Wani mazauni garin na Kabalewa ya shaidawa RFI Hausa cewa wasu mata ne guda biyu suka shiga sansanin ‘yan gudun hijira suka tarwatsa kansu, kuma harin ya kashe mutane biyu da jikkata wasu da dama.

Ya ce Matan sun kai harin ne a Masallacin sansanin na ‘yan gudun hijira.

Jihar Diffa dai na cikin dokar ta-baci da gwamnatin Nijar ta kafa domin yaki da ‘yan Boko Haram da suka jima suna kai hare hare a yankin.

Dubban ‘yan gudun hijirar rikicin Boko Haram daga Najeriya ne suka tsallaka zuwa Nijar yawancin daga jihohin Yobe da Borno da ke makwabtaka da Diffa.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2017)
پیام امام خامنه ای به مسلمانان جهان به مناسبت حج 2016
We are All Zakzaky