Boko Haram Suka Kashe Sojojin Niger Sama Da Bakwai

Boko Haram Suka Kashe Sojojin Niger Sama Da Bakwai

Gwamnatin jamhuriyar Nijer ta tabbatar da mutuwar sojojinta 7 da kuma jikkatar wasu 17 na daban sanadiyar harin da mayakan boko haram suka kai musu a jahar Diffa dake kudu maso gabashin kasar.

A cikin wata Sanarwa da Ma'aikatar harakokin tsaron kasar ta Nijer ta fitar a jiya juma'a ta tabbatar da mutuwar sojoji 7 tare da jikkatar wasu 17 na daban a harin da mayakan kungiyar Boko haram suka kai musu a yankin Toummour dake cikin jahar Diffa na kudu maso gabashin kasar.

Sanarwa ta ce an kai harin ne a daren Laraba wayewar garin Alhamis kuma daya daga cikin sojojin ya bace , sai dai gwamnati ba ta yi karin haske ba game da yadda aka kai harin.

Wannan dai ba shi ba ne karo na farko da mayakan boko haram din ke kai hari a yankin na Toummour mai iyaka da na Najeriya, inda ko a ranar 3 ga watan yunin 2016, mayakan na boko haram sun kai hari garin tare da kashe sojojin Nijer 26 tare da wasu farar hula da dama.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky