Boko Haram: Sojojin Nigeria 30 Sun Hallaka

Boko Haram: Sojojin Nigeria 30 Sun Hallaka

Rahotanni daga Najeriya na cewa akalla dakarun Sojin kasar 30 ne suka mutu yayin wata fafatawarsu da mayakan Boko Haram a yankin arewa maso gabas da ke gab da kan iyakar kasar da Jamhuriyyar Nijar.

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya nakalto majiyar tsaron Najeriya a wannan asabar na cewa akalla sojoji 30 ne suka mutu a wani farmaki da mayakan boko haram suka kai sansaninsu dake kan iyaka da jamhuriyar Nijar.

A cewar majiyar tun a ranar Alhamis ne wani adadi mai yawa na Mayakan Boko Haram  yayi  dirar mikiya kan sansanin Sojin Najeriyar da ke kauyen Zari a arewacin jihar Borno gab da kan iyaka da jamhuriyar Nijar, kuma bayan daukar tsawon lokaci ana fafatawa mayakan suka yi nasara fatattakar dakarun sojin tare da hallaka kusan 30 da kuma jikkata wani adaidi mai yawa daga cikinsu.

A baya-bayan nan dai ana yawan samun kai farmaki kan dakarun sojin wanda a lokuta da dama akan kashe su tare da tarwatsa wasu zuwa cikin dazuka, inda ko a kwanakin baya wasu sojojin sun bace a daji duk da cewa shalkwatar rundunar sojin Najeriyar ta musanta hakan.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky