Boko Haram: An Gaddamar Da Wani Hari A Yobe

Boko Haram: An Gaddamar Da Wani Hari A Yobe

Wasu 'yan bindiga da ake zargin mayakan Boko haram ne sun kai hari a garin Katarka na kusa da garin Damaturu na jihar Yobe dake shiyar arewa maso gabashin Najeriya.

Rahotanni daga fitowa  daga tarayyar Najeriya na cewa  'yan bindiga sun kai harin ne da misalin karfe 5 na yammacin jiya Laraba a garin Katarko da ke kusa da garin na  Damaturu a jahar ta Yobe.

Maharan sun buda wuta kan mai uwa da wabi, lamari da ya sanya al'ummar garin suka banzama cikin dajuka, 

Ya zuwa yanzu babu wata sanarwa da ta fito daga jami'an tsaro ko gwamnati a game da wannan hari.

Jihar Yobe dai na daga cikin jihohin yankin arewa maso gabashi da suka dade suna fama da hare haren  kungiyar ta'addancin nan ta Boko Haram.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky