Birtaniya:Takunkumin Kasar Amurka Kan Iran Ba Zai Yi Tasiri Ba

Birtaniya:Takunkumin Kasar Amurka Kan Iran Ba Zai Yi Tasiri Ba

Mataimakin sakataren harkokin wajen kasar Birtaniya ya ce: Takunkumin da kasar Amurka ta kakaba kan kasar Iran ba zai yi wani gagarumin tasiri ba.

A zantawarsa da kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran: Mataimakin sakataren harkokin wajen kasar Birtaniya Alistair Burt ya bayyana cewa: Matakin da kasar Amurka ta dauka na sake dawo da takunkumin da ta kakaba kan kasar Iran lamari ne da ba zai yi tasiri ba musamman matakin da kasashen yammacin Turai suka dauka na kin amincewa da matsayar kasar ta Amurka.

Burt ya kara da cewa: Kasashen yammacin Turai da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar nukiliyar kasar Iran sun jaddada matsayinsu na ci gaba da yin aiki da yarjejeniyar sakamakon haka zasu ci gaba da gudanar da harkarsu ta tattalin arziki da kasar ta Iran.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky