Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ya Bukaci Kawo Karshen Yaki A Kasar Yamen

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ya Bukaci Kawo Karshen Yaki A Kasar Yamen

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci kawo karshen kai hare-hare ta sama da kasa kan kasar Yamen tare da hanzarta aikewa da kayayyakin jin kai zuwa kasar.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya watsa rahoton cewa: Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres a jiya Lahadi ya yi gargadin cewa: Hare-haren wuce gona da iri da ake kai wa kan kasar Yamen tare da killace kasar ta sama da kasa da kuma ta ruwa sun wurga al'ummar kasar cikin mummunan kangi musamman bullar masifar yunwa, cututtuka da hasarar rayukan jama'a musamman kananan yara.

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana tsananin damuwarsa kan yadda masarautar Saudiyya da kawayenta suke ci gaba da kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan al'ummar Yamen, don haka ya jaddada yin kira kan kawo karshen wannan rashin dan Adamtaka.

Rahotonni daga Yamen suna nuni da cewa: Jiragen saman yakin masarautar Saudiyya da na kawayenta sun tsananta kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan birnin Sana'a fadar mulkin kasar ta Yamen a cikin 'yan kwanakin nan musamman ganin yadda aka samu baraka a tsakanin dakarun sa-kai na kungiyar Ansarullah ta mabiya Huthi da na magoya bayan tsohon shugaban kasar Ali Abdullahi Salih. 


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky