Babban Sakataren Kungiyar Ansarullahi Ta Yamen Ya Yi Gargadi Kan Fitinar Da Ta Kunno Kai A Kasar

Babban Sakataren Kungiyar Ansarullahi Ta Yamen Ya Yi Gargadi Kan Fitinar Da Ta Kunno Kai A Kasar

Babban sakataren kungiyar Ansarullahi ta mabiya Huthi ya yi kira ga al'ummar Yamen da su fadaka kan makircin da mahukuntan Saudiyya suke kitsawa da nufin hada al'ummar Yamen fada a tsakaninsu.

A jawabin da ya gabatar a yau Asabar ta hanyar kafar talabijin: Babban sakataren kungiyar Ansarullahi ta mabiya Huthi Badruddeen Huthi ya yi suka kan matakin da wasu mabiya tsohon shugaban kasar Abdullahi Salihu suka dauka na kokarin kunna wuta yaki tsakanin kungiyoyin da suke kawance a tsakanin da nufin yakar sojojin mamayar masarautar Saudiyya da kawayenta: Yana mai bayyana cewa: Sojojin Abdullahi Salihu suna aiwatar da wasu munanan halaye da suke sanya kokwanto kansu, don haka yana kira gare su da su hanzarta kawo karshen wadannan halaye.

Har ila yau Badruddeen Huthi ya yi kira ga dukkanin al'ummar Yamen da masana gami da kungiyoyi na kasar da su hanzarta daukan matakin shiga tsakani domin warware rikicin da ya kunno kai a birnin Sana'a fadar mulkin kasar ta Yamen tsakanin 'yan kungiyarsa ta Ansarullah da sojojin tsohon Shugaban kasar Abdullahi Salihu.

Rahotonni suna bayyana cewa: Dauki ba dadi tsakanin 'yan kungiyar Ansarullah da sojojin Abdullahi Salihu a birnin Sana'a fadar mulkin kasar ya lashe rayukan mutane fiye da 100, kuma rikici tsakanin bangarorin biyu ya kunno kai ne bayan da sojojin Abdullahi Salihu suka zargi mabiyan kungiyar Ansarullahi da ta da bom a yankin kudancin birnin Sana'a fadar mulkin kasar.  


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky