Ayatullah Khamene'i: Amurka Ta Tafka Kura-Kurai Masu Yawa Kan Birnin Qudus Na Palasdinu

Ayatullah Khamene'i: Amurka Ta Tafka Kura-Kurai Masu Yawa Kan Birnin Qudus Na Palasdinu

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya bayyana cewa: Matakin da kasar Amurka ta dauka kan birnin Qudus na Palasdinu, babban kuskure ne amma ba zata iya aiwatar da wannan kuskuren ba a aikace.

A jawabinsa ga mahalatta zaman taron Majalisun Dokokin Kasashen Musulmi na kungiyar O.I.C karo na 13 da ake gudanarwa a Jamhuriyar Musulunci ta Iran, a yammacin jiya Talata: Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Sayyid Ali Khamene'i ya bayyana matsalar Palasdinu a matsayin matsalar da tafi addabar duniyar musulmi: Yana mai fayyace cewar matsalar mamaye yankunan Palasdinawa da tilatawa miliyoyin Palasdinawa yin gudun hijira da kuma aiwatar da kisan gilla kansu, ayyukan zalunci ne da ba a taba ganin makamantansu a tsawon tarihi ba.

Jagoran juyin juya halin na Musulunci ya kara da cewa: Kare hakkokin Palasdinawa; hakki ne da ya rataya a wuyar dukkanin al'umma, don haka kuskure ne tunanin cewa kalubalantar yahudawan sahayoniyya 'yan mamaya bata amfani musamman idan aka yi la'akari da irin yadda gwagwarmayar Palasdinawa ta samu gagarumar nasara a shekarun baya-bayan nan.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky