AU Na Goyon Bayan Sulhun Habasha Da Eritrea

AU Na Goyon Bayan Sulhun Habasha Da Eritrea

Shugaban hukumar tarayyar Afirka Musa Faki Muhammad ne ya bayyana goyon bayan ga kokarin warware sabani a tsakanin kasashen Habasha da Eritrea

Kamfanin dillancin labarun Xinhua ya ambato Musa Faki Muyhammad Yana cewa; Sauye sauyen da ake samu a gabacin Afirka na sulhu tsakanin kasashe abin a yaba da shi ba.

Kasashen Habasha da Eritrea sun mayar da huldar diplomasiyya a tsakaninu a ranar 16 ga watan Yuni wanda shi ne na farko a cikin shekaru ashirin na alakar kasashen biyu mai cike da sabani.

Shugaban  kasar Eritrea  Isaias Afewerki ne ya halarci bikin bude ofishin jakadancin kasar tashi a Addis Ababa.

Ita ma kasar Habashan ta tura jakadanta na farko Rezvan Husain zuwa kasar Eritrea a ranar 19 g awatan na Yuni.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky