Ana Zargin Saudiyya Da Kulla Juyin Mulki A Tunisiya

Ana Zargin Saudiyya Da Kulla Juyin Mulki A Tunisiya

Wata kafar watsa labaran Tunusiya ta fallasa makircin masarautar Saudiyya na kokarin sake dawo da hambararren shugaban kasar dan kama karya kan karagar shugabancin Tunusiya.

Shafin watsa labaran Arra'ayi Tunusiya ya watsa labarin cewa: Masarautar Saudiyya tana kokarin sake dawo da hambararren shugaban kasar Tunusiya dan kama karya Zainul-Abideenbin Ali kan karagar shugabancin kasar.

Shafin na Arra'ayi Tunusiya ya kara da cewa: Tsohon ministan harkokin cikin gidan kasar Tunusiya Lutfi Barham a ranar 25 ga watan Fabrairun wannan shekara ya gudanar da zaman tattaunawa da mahukuntan Saudiyya musamman ministan harkokin cikin gidan Saudiyya da ministan harkokin wajen kasar Adil Jubair da kuma tawagar hukumar leken asirin kasar ta Saudiyya kan batun matakan sake dawo da Zainul-Abideen kan karagar shugabancin kasar Tunusiya.

Tun bayan boren da ya kunno kai a kasashen Larabawa wanda tushensa kasar ta Tunusiya ce a shekara ta 2011 ya kawo karshen mulkin kama karya na Zainul-Abideenbin Ali da ya shafe tsawon shekaru 24 yana mulki a Tunusiya, inda ya tsere Saudiyya tare da samun mafaka a kasar. 


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky