Ana Gudanar Da Gagarumar Zanga-Zangar Goyon Bayan Gwamnati A Halin Yanzu A Nan Tehran

Ana Gudanar Da Gagarumar Zanga-Zangar Goyon Bayan Gwamnati A Halin Yanzu A Nan Tehran

Bayan Sallar Jumma'a a nan Tehran, dubban dubatan mutanen a nan birnin Tehran zasu gudanar da gagarumar zanga zanga don nuna goyon bayansu ga tsarin musulunci da ke gudanar da kasar da kuma yin Allah wadai da masu tada fitina.

Kwamitin shirya zanga zangar a nan Tehran ya bada labarin cewa Malaman addini, da maraji'ai da shuwagabannin yankuna da kuma  yan siyasa duk sun bukaci mutanen birnin Tehran su fi don gudanar da wannan zanga-zangar a yau Jumma'a bayan sallar Jumma'a.

Labarin ya kara da cewa fara zanga zangar a wurare 40 a cikin birnin na Tehran, inda masu zanga zangar zasu sake jaddada bai ga jagoran juyin juya halin musulunci kasar da kuma tsarin da ke jagorantar kasar kimani shekaru 40 da suka gabata.

A ranar 28 ga watan Decemban da ta gabata ce wasu masu son tada fitina suka tada tarzoma wanda ya kai ga kate hurumin addini da kuma munana jumhuriyar musulunci . Har'ila yau wanda ya kai ga asarar rayuaka da dukiyoyi.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky