Ana ci gaba da gwabza fada a gabashin Tripoli na Libya

Ana ci gaba da gwabza fada a gabashin Tripoli na Libya

An samu barkewar kazamin fada a gabashin Tripoli tsakanin dakarun da ke biyayya ga gwamnatin da ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya da kuma gwamnatin ‘yan adawa a Garabulli.

Rahotanni sun ce rikicin ya barke ne tsakanin dakarun da ke biyayya ga tsohon Firaminista Khalifa Ghweil wanda ya ki amincewa da gwamnatin hadin kai da ke samun goyan bayan Majalisar Dinkin Duniya.

Rundunar Majalisar Dinkin Duniya da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Libya ta fito ta yi watsi da farmakin wanda ta kira hari akan Tripoli.

An hambarar da Ghweil ne daga madafan ikon Libya bayan kafa gwamnatin hadin kai a watan Maris na 2016.

Fafatwar ta dada fito da rashin goyan bayan da Gwamnatin hadin kan ke samu daga wasu bangarori.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Quds cartoon 2018
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2017)
پیام امام خامنه ای به مسلمانان جهان به مناسبت حج 2016
We are All Zakzaky