An Yi Ganawar Sirri A Tsakanin Natanyahu Da Jakadan Hadaddiyar Daular Larabawa A Amurka

An Yi Ganawar Sirri A Tsakanin Natanyahu Da Jakadan Hadaddiyar Daular Larabawa A Amurka

Kamfanin dillancin labarun Associated Press ya ba da labarin cewa; A cikin watan Maris da ya gabata ne aka yi ganawar a tsakanin Natanyahu da Yusuf al-Utaibi, jakadan Hadadddiyar Daular Larabawa a Amurka.

rahoton ya kara da cewa an yi ganawar ne a karkashin shiga tsakanin -Brian Hook wanda jami'i ne a ma'aikatar harkokin wajen Amurka.

Bugu da kari ganawar ta kunshi ministan harkokin waje na kasar Bahrain, Shekih Abdullah Bin Rashid ali-Khalifah.

Ganawar dai ta zo ne a daidai lokacin da shugaban Amurka Donald Trump ya ambata cewa wasu daga cikin kasashen larabawa sun amiince da matakin da ya dauka na ficewar kasarsa daga yarjejeniyar Nukiliya.

Kawo ya zuwa yanzu kasashen na Daular Larabawa da Bahrain ba su ce uffan ba akan rahoton na Associated Press.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky