An yankewa wasu 'yan uwa Musulmi na Misra hukuncin kisa

An yankewa wasu 'yan uwa Musulmi na Misra hukuncin kisa

Kotun da ke shari'ar manyan laifuka ta birnin Alkahira na kasar Masar ta yanke hukuncin kisa kan 'yan kungiyar Ihwanul-Muslimin su 75 tare da zartar da hukuncin daurin rai da rai a gidan kurkuku kan wasu 46 na daban.

Bayan tuntubar Muftin Masar da samun ra'ayinsa; Kotun da ke shari'ar manyan laifuka ta birnin Alkahira na kasar ta Masar a yau Asabar ta yanke hukuncin kisa kan 'yan kungiyar Ihwanul-Muslimin su 75 da ake zargi da hannu a tarzomar dandalin Rabi'atul-Adwiyyah bayan kifar da gwamnatin Muhammad Morsi a shekara ta 2013.

Mutane 29 daga cikin 75 da kotun ta yanke musu hukuncin kisar, ba su hallara a gaban kotun ba saboda har yanzu mahukuntan kasar ba su kai ga kama su ba, don haka aka yanke musu hukuncin a bayan idonsu. Kamar yadda kotun ta zartar da daurin rai da rai a gidan kurkuku kan wasu 'yan kungiyar ta Ihwan su 46 na daban.

Tun a ranar 14 ga watan Agustan shekara ta 2013 ne sojojin gwamnatin Masar suka farma jama'ar da suka taru a dandalin Rabi'atul-Adwiyyah da na Annahdhah da suke birnin Alkahira domin nuna rashin amincewarsu da kifar da gwamnatin Muhammad Morsi da aka yi lamarin da ya haifar da tarzoma da ta yi sanadiyyar mutuwar daruruwan mutane tare da jikkatan wasu adadi mai yawa na daban.     


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky