An Yanke Hukuncin Daurin Rai Da Rai Ga Jagoran Kungiyar 'Yan Uwa Musulmi

An Yanke Hukuncin Daurin Rai Da Rai Ga Jagoran Kungiyar 'Yan Uwa Musulmi

Kotun Hukunta manyan Laifuka ta Kasar Masar ta yanke hukuncin daurin rai da rai ga jagoran kungiyar 'yan Uwa musulmi

Kamfanin dillancin Arabie News ya habarta cewa a jiya Litinin kotun hukunta manyan laifuka ta kasar Masar ta yanke hukuncin daurin rai da rai ga Muhamad Badi'i Shugaban Kungiyar Jama'atu Ikhwanul-musulmin kan zarkinsa da hannu a zaman dirshin din da magoya bayan kungiyar Jama'atu Ikhwanul-musulmin suka yi a gaban masallacin Rabi'atul-Adawiya dake birnin Alkahira.

Har ila yau kotun ta yanke irin wannan hukunci ga wasu jiga-jigan kungiyar guda biyu sannan ta yankewa wasu magoya bayan kungiyar ta 'yan uwa musulmi 15 daurin shekaru biyar a gidan yari.

A watan Avrilun shekarar 2015 din da ta gabata wata kotun hukunta manyan laifuka ta kasar ta yankewa magoya bayan kungiyar ta 'yan uwa musulmi 13 hukuncin kisa kan zarkin su da hanu a zaman dirshin din da magoya bayan kungiyar Jama'atu Ikhwanul-musulmin suka yi a gaban masallacin Rabi'atul-Adawiya, saidai kotun daukaka kara ta watsi da wannan hukunci sannan ta bukaci da a sake gurfanar da su a wata kotun hukunta manyan laifuka ta daban.

Bayan kifar da Gwamnatin Muhamad Mursi a shekarar 2013, an haramta aiyukan kungiyar Jama'atul Ikhwanul-musulmin wacce da kawo shi kan karagar milki tare kuma da kame adadi mai yawa daga cikin jiga-jigan kungiyar da magoya bayan ta tare da daure su a gidan kaso.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Quds cartoon 2018
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2017)
پیام امام خامنه ای به مسلمانان جهان به مناسبت حج 2016
We are All Zakzaky