An Sanar Da Rasuwar Tsohon Shugaban Kungiyar Ikhwanul Muslim Mahdi Aakif

An Sanar Da Rasuwar  Tsohon Shugaban Kungiyar Ikhwanul Muslim Mahdi Aakif

Tsohon shugaban kungiyar ikhwanul - muslimin ta kasar Masar ya rasu a cikin kurkuku

Tashar television ta Al-alam a nan Tehran ta nakalto wakilin kungiyar a birnin Alkahira Muntasar Azziyaat yana fadar haka a jiya Asabar, ya kuma kara ta cewa Mahdi Aakif ya rasu yana dan shekara 88 a duniya.

Akif ya rike shugabancin kungiyar ne a shekara ta 2004 bayan rasuwar Mamin al-hudaibi, bayansa ne Mohammad Badee ya maye gurbinsa.

Gwamnatin kasar masar ta yanzu dai ta yi amfani da karfin da wace misali kan y'ay'an kungiyar ta Ikhwanul muslimin sannan ta hana fursinoninsu samun magani ko ganin likitoci a lokacinda suke cikin gidan yari.

Aakif yana daga cikin fursononin da aka yenkewa hukuncin daurin rai da rai bayan juyin mulki, da kuma rikicin da suka biyo bayan rikicin shekara ta 2013.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Quds cartoon 2018
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2017)
پیام امام خامنه ای به مسلمانان جهان به مناسبت حج 2016
We are All Zakzaky