An samu sojoji da laifin yi wa mata masu aikin agaji fyade

An samu sojoji da laifin yi wa mata masu aikin agaji fyade

Wata kotun soji a Sudan Ta Kudu ta samu sojoji 10 da laifin yi wa ma'aikatan agaji fyade tare da kashe wani dan jarida.

Kotun ta kuma umarci gwamnatin Sudan ta Kudu ta biya kowa cikin wadanda aka yi wa fyaden dala dubu 4 (naira miliyan 1.2) a matsayin diyya.

An aikata laifukan ne a lokacin da aka kai samame otel din Terrain Hotel a babban birnin kasar, Juba a shekarar 2016.

An zargi sojojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya da ke kusa da kasa kai dauki a lokacin da ake neman taimakonsu. An gabatar da hukuncin ne a wata kotun soji makere da jami'an diflomasiyya da kuma ma'aikatan ba da agaji.

An wanke wani soja daga aikata laifi yayin da wani soja kuma ya mutu.
ko
An kaddamar da harin ne a yayin da ake fafatawa tsakanin dakarun gwamnati da 'yan tawaye a Juba.

An kashe sama da mutum 70, ciki har da sojojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya.

Kotun ta bai wa gwamnati umarnin biyan dan Birtaniya mai oten din, Mike Woodward, dala miliyan 2 ( naira miliyan 612).


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky