An saki wasu ‘Yan shi’a mabiya Sheikh Zakzaky da kama a 2015

An saki wasu ‘Yan shi’a mabiya Sheikh Zakzaky da kama a 2015

An saki wasu ‘Yan shi’a mabiya Sheikh Zakzaky da kama a 2015

A yau Alhamis 9 ga watan Nuwamba, Wani Alkali a babban kotun jihar Kaduna yayi watsi da wata kara da gwamnatin jihar Kaduna ta shigar tana zargin wasu ‘yan shi’a mabiya Sheikh Ibrahim Zakzaky da tashin tashena, haramtaccen taro,da kuma zagon kasa ma zaman lafiya.
Su wa’yannan bayin Allah su kimanin goma an kama su ne a yayin wata jerin gwano da aka gabatar a ranar talata 15 ga watan Disambar shekarar 2015, domin nuna rashin amincewa da ta’addancin da sojoji suka aiwatar a kan Sheikh Zakzaky daga ranar 12 zuwa 14 na Disambar 2016 a garin Zariya.
Alkalin ya bayyana cewa yayi watsi da karar ne saboda rashin gamsassun hujjoji akan zargin da ake ma wa’yannan bayin Allah na tayar da tarzoma da sauran tuhumomin da ake masu.
Majiyarmu ta shaida mana cewa daga cikin wa’yanda aka saka a yau bayan shafe fiye da watanni 20 a gidan yarin jihar Kaduna akwai Malam Aliyu Bakin Ruwa, Malam Sani Mai Sanda, Malam AlBashir Aljazari da sauransu.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky