An Rantsar Da Sabon Shugaban Kasar Zimbabuwe

An Rantsar Da Sabon Shugaban Kasar Zimbabuwe

Mnangagwa ya sha alwashin kafa "sabuwar Zimbabwe" bayan ya yi rantsuwar kama aiki a matsayin sabon shugaban kasar.

Kazalika ya sanar da kafa kwamitin da zai yi bincike kan mutuwar mutum shida a taho-mu-gamar da aka yi tsakanin sojoji da 'yan hamayya bayan zaben da aka yi a watan Yuli.

Ya ce hatsaniyar abin takaici ne.

Gamayyar jam'iyyun hamayya ta MDC ta ci gaba da yin watsi da sakamakon zaben duk da hukuncin da kotu ta yi na tabbatar da sahihancinsa.

Zaben na watan Yuli shi ne na farko da aka gudanar tun bayan da aka kawar da tsohon shugaban kasar Robert Mugabe daga kan mulki.

Shugaban MDC Nelson Chamisa ya ce an yi magudi a zaben kuma bai halarci bikin rantsuwar kama aiki da Mr Mnangagwa ya yi ba.

Ya kara yin tur da rikicin da ya auku bayan zaben, yana mai cewa "bakon abu ne ha 'yan Zimbabwe" kana ya mika ta'aziyyarsa ga iyalan mutanen da suka mutu.

Mr Mnangagwa ya bayyana kan sa a matsayin "shugaban da ke jin koke-koken jama'a", inda ya kara da cewa gwamnatinsa za ta mayar da hankalin wurin yin biyayya ga kundin tsarin mulkin kasar da bayar da 'yanci ga bangaren shari'a.

" Muna son kafa kasar Zimbabwe wacce ba ruwan ta da ata jam'iyya," in ji shi.

Mr Mnangagwa - dan jam'iyyar Zanu-PF ta tsohon shugaba Mr Mugabe ne - kuma ya sha alwashin kawo sauyi a fannin tattalin arzikin inda za a samu masu zuba jari daga gida da wajen kasar.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky