An kama wani ɗan Boko-Haram a Jamus

An kama wani ɗan Boko-Haram a Jamus

Hukumomin ƙasar Jamus sun sanar da kama wani mutumin Najeriya mai suna Amaechi da ake zargin ɗan kungiyar Boko-Haram ne.

Ana zargin cewa mutumin ya taimaka wajen kai hare-hare a makarantu da ƙauyukan jihar Borno ta arewacin Najeriya.

Alƙalin wata kotu a ƙasar, tuni ya bayar da umurnin tsare mutumin mai suna Amaechi Fred O. a wani gidan yari da ke Bavaria.

Sanarwar da gwamnatin Jamus ɗin ta bayar ta ce Amaechi ya amsa cewa yana da hannu wajen kai hare-hare har guda 4 a kan fararen hula cikin shekara 1 da ya yi a matsayin ɗan ƙungiyar ta Boko Haram.

Yanzu haka ana tuhumar sa da laifin kashe mutane da dama, daga ciki har da daliban makaranta.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky