An Kai Harin Ta'addanci A Wani Masallaci A Kasar Afrika Ta Kudu

An Kai Harin Ta'addanci A Wani Masallaci A Kasar Afrika Ta Kudu

Wasu mahara sun kai farmaki cikin wani Masallaci a shiyar kudu maso yammacin kasar Afrika ta Kudu, inda suka kashe mutane biyu.

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya watsa labarin cewa: Wasu mahara sun kai farmaki cikin wani Masallaci a garin Malmezebury da ke kusa da jihar Cape Town a shiyar kudu maso yammacin kasar Afrika ta Kudu, inda suka soke mutane biyu da wuka har lahira tare da jikkata wasu adadi masu yawa.

Jami'an 'yan sandan Afrika ta Kudu sun samu nasarar hanzarta kawo dauki Masallacin, inda suka harbe maharan biyu har lahira. Rundunar 'yan sandan jihar Cape Town ta fara gudanar da bincike domin gano dalilin maharan na kai hari cikin Masallacin.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky