An Kai Harin Kunan Bakin Wake A Kasar Tunusiya

An Kai Harin Kunan Bakin Wake A Kasar Tunusiya

Wata Mata da ta yi jigida da bama-bamai ta tarwatsa kanta a kusa da ma'aikatar cikin gida ta kasar Tunusiya

Kafafen yada labaran kasar Tunusiya sun habarta cewa a wannan litinin wata Mata da tayi jigida da bama-bamai ta tarwatsa a kanta a kusa da wata tawagar jami'an tsaron sintiri kan titin Habib Bourguiba dake kusa ma'aikatar cikin gidan kasar a Tunus babban birnin kasar.

Ma'aikatar cikin gidan Tunusiya ta tabbatar da wannan labari, kuma ta ce an kai harin ne da nufin kashe jami'an 'yan sandar dake sunturi domin tabbatar da tsaro gami da kare rayukan Al'umma. 

Har ila yau ma'aikatar cikin ta tunusiya ta tabbatar da jikkatar mutane 9 sanadiyar wannan hari, inda ta ce an gano wacce ta kai hari mai shekaru kimanin 30 a Duniya.

Wasu kafafen yada labaran Tunusiyar sun tabbatar da cewa mahariyar 'yar asalin kasar Tunusiya ce.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky