An Kai Hari A Jami'ar Mombasa Da Ke Kasar Kenya

 An Kai Hari A Jami'ar Mombasa Da Ke Kasar Kenya

Rundunar 'yan sandan kasar Kenya ta sanar da cewa: Wasu gungun mahara sun kai harin wuce gona da iri kan jami'ar Mombasa da kudancin kasar Kenya, inda suka kashe mutane biyu tare da jikkata wasu na daban.

Majiyar rundunar 'yan sandan Kenya ta sanar da cewa: Wasu gungun mahara sun kaddamar da harin wuce gona da iri kan jami'ar Mombasa da ke kudancin kasar a yau Talata, inda suka kashe mata biyu ma'aikata a jami'ar tare da jikkata wasu dalibai masu yawa.

Maharan sun samu nasarar tserewa amma tuni aka nuna yatsar zargin kan mayakan kungiyar ta'addanci ta Al-Shabab na kasar Somaliya da suka yi kaurin suna wajen kai hare-haren wuce gona da iri kan makarantu da jami'o'i a kasar Kenya. 


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

mourning-of-imam-hussain
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky