An Kafa Wata Kotu Da Zata Gudanar Da Shari'ar Tsoffin Shugabannin Kasar Afrika Ta Tsakiya

An Kafa Wata Kotu Da Zata Gudanar Da Shari'ar Tsoffin Shugabannin Kasar Afrika Ta Tsakiya

Mahukunta a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya sun sanar da cewa: An kafa wata kotu ta musamman da zata gudanar da shari'a kan tsoffin shugabannin kasar guda biyu dangane da zargin hannu a kunna wutan yakin basasa a kasar.

Rahotonni daga Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya suna bayyana cewa: Kotun ta musamman ta fara gudanar da zamanta ne a ranar Litinin 22 ga wannan wata na Oktoba a birnin Bangui fadar mulkin kasar da nufin gurfanar da tsoffin shugabannin kasar biyu Francois Bozize da Michel Djotodia kan zargin hannu a kunna wutan yakin basasa a kasar.

Har ila yau yana daga cikin ayyukan kotun ta musamman gudanar da bincike kan laifukan yaki da aka tafka a kasar tun daga shekara ta 2003 zuwa 2013 tare da gurfanar da mutanen da suke da hannu a tafka laifukan a gaban kotu domin hukunta su.

Tun a shekara ta 2013 ne Majalisar Dinkin Duniya ta gabatar da shawarar kafa kotu ta musamman a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya da nufin binciko masu hannu a tafka laifukan yaki a kasar musamman a tsakanin mayakan kungiyoyin da suke dauke da makamai na Seleka ta mabiya addinin Musulunci da Anti-Balaka ta mabiya addinin Kirista. 


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky