An Gudanar Da Zanga Zangar Yin Allah Wadai Da Masu Tayar Da Fitina A Fadin Kasar Iran

An Gudanar Da Zanga Zangar Yin Allah Wadai Da Masu Tayar Da Fitina A Fadin Kasar Iran

Dubun dubatar Iraniyawa a dukkanin biranen kasar a halin yanzu suna gudanar da zanga zangar nuna goyon bayan tsarin musulunci da kuma gwamnatin kasar.

Tashar talabijin ta Presstv ta habarta cewa,  an shiya zanga zangar ne a safiyar yau Laraba kuma mutanen daga yan kasuwa ma'aikatan gwamnati da masu zaman kansu sun shiga cikin zanga zangar ta nuna goyon baya ga tsarin musulunci wanda yake jagorantar kasar da kuma yin Allah wadai da wadanda suke son tada fitina a cikin yan kwanakin da suka gabata a kasar.

A cikin makon da ya gabata ne wasu mutane suka fara zanga zanga a wasu biranen kasar don nuna damuwarsu kan karin farashin wasu kayayyakin masarufi da wasu akmfanoni suka yi a kasar, tare da kokwa ga gwamnati kan lamarin, amma wasu wadanda suke da mummunar manufa suka janye ragamar zanga zangar zuwa nuna kiyayya ga tsarin musulunci da ke jagorantar kasar. Har'ila hakan ya jawo mutuwar mutane da kone-konen wuraren gwamnati da na sauran jama'a


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Arba'een
mourning-of-imam-hussain
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky