An Gudanar Da Janazar Shugaban Majalisar Koli Ta Siyasa Ali Samad A San'a Ta Yeman

An Gudanar Da Janazar Shugaban Majalisar Koli Ta Siyasa Ali Samad A San'a Ta Yeman

Dubbar daruruwan jama'a ne a birnin Sana' na kasar Yemen suka halarci janazar shugaban majalisar koli ta siyasa a kasar Yemen Saleh Ali Samad, wanda Saudiyyah tare da hadin gwiwa da Amurka suka yi kisan gilla a ranar Alhamis ta wancan makon da ya gabata.

Kamfanin dillancin labaran Mehr ya bayar da rahoton cewa, a lokacin da dubban daruruwan mutane suke gudanar da janazar shugaban majalisar koli ta siyasa  a kasar ta Yemen Saleh Samad a yau a birnin San'a, jiragen yakin Saudiyya sun kai hare-hare a kusa da wurin da ake taron janazar, yayin da dakarun kasar gami da sojin sa kai su kuma suka mayar da martani da makamai masu linzami guda 8 a wasu sansanonin sojin Saudiyya da ke yankin Jizan a kudancin kasar.

A cikin kasa da mako guda da ya gabata, Saudiyya ta kashe fararen hula fiye da sattin a cikin kasar Yemen, daga ciki kuwa har da harin da ta kai a ranar Litinin a kan taron bikin aure, inda ta kashe mutane 33, da suka hada har da amraya, lamarin da ya fusata al'ummomin duniya da dama.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky