Kotun da ke sauraren shari'ar sheikh Ibrahim Zakzaky jagoran harkar musulunci a Najeriya ta sanar da dage zaman shari'ar har zuwa ranar 7 ga watan Nuwamba.
Rahotanni daga Najeriya sun ce a yau ne 4 ga watan Oktoban 2018 ake gudanar da zaman sauraren shari'ar sheikh Ibrahim Zakzaky a garin Kaduna, sai dai kotun ta sanar da dage zaman sauraren shari'ar har zuwa 7 ga watan Nuwamba mai kamawa, bayan da masu shigar da kara suka bukaci hakan,
Masu shigar da karar dai sun gaya wa kotun cewa a yau ne shugaban kasa Muhammad Buhari zai ziyarci Kaduna, saboda dalilai na tsaro suka bukaci a dage zaman shari'ar, kuma kotu ta amince da hakan.
Gwamnatin jahar Kaduna ce dai ta shigar da karar a kan sheikh Ibrahim Zakzaky da mai dakinsa Malama Zinatu Ibrahim, da kuma Sheikh Yakubu Yahaya Katsina da kuma Malam Sanusi Abdulkadir, bisa zarginsu da kashe soja guda a lokacin da sojoji suka kai farmaki a kan gidan Sheikh Ibrahim Zakzaky a Zaria a cikin watan Disamban 2015.
Harkar musulunci ta zargi sojojin Najeriya da yin kisan gilla a kan mabiya Harkar su kimanin 1000 a lokacin farmakin da suka kai kan gidan Sheikh Zakzaky, yayin da su kuma sojoji suke cewa adadin bai haka ba.