An Ci Gaba Da Zanga-Zangar Neman A Saki Sheikh Zak zaky

An  Ci Gaba Da Zanga-Zangar Neman A Saki Sheikh Zak zaky

Magoya bayan Harkar Musulunci a Nigeriya suna ci gaba da gudanar da zanga-zangar lumana da taron gangami a birnin Abuja fadar mulkin tarayyar Nigeriya domin neman sakin shugabansu Sheikh Ibrahim Yakub El-Zakzaki

Daruruwan magoya bayan Harkar Musulunci a Nigeriya suna ci gaba da gudanar da zanga-zangar lumana da taron gangami a birnin Abuja fadar mulkin kasar da nufin tursasawa gwamnatin kasar mutunta umurnin kotu da ta zartar da hukuncin sakin jagoransu Sheikh Ibrahim Yakub El-Zakzaki.

Har ila yau magoya bayan Harkar Musuluncin a jiya Laraba sun yi zaman dirshen a kofar Majalisar Dattijan Nigeriya, inda suka gabatar da kokensu ga Majlisar musamman matakin da gwamnatin Muhammadu Bukhari ta dauka na rashin biyayya ga umurnin kotu.

Tun a watan Disamban shekara ta 2015 ce sojojin gwamnatin Nigeriya suka farma mabiya Harkar Musulunci a garin Zariya da ke jihar Kaduna, inda suka kashe daruruwan mutane tare da rusa gidan Sheikh Ibrahim Yakub El-Zakzaki da cibiyar harkokin addinin Musulunci ta Harkar Musuluncin, kuma har yanzu akwai magoya bayan harkar a gidajen kurkuku musamman a garin Kaduna.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky