An Bukaci A Gudanar Da Bincike Kan Kisan Da HK, Isra'ila Ta Yi Wa Palastinawa A Gaza

An Bukaci A Gudanar Da Bincike Kan Kisan Da HK, Isra'ila Ta Yi Wa Palastinawa A Gaza

Babban sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterres ya bukaci da a gudanar da bincike dangane da kisan da sojojin Isra'ila suka yi kan Palastinawa a jiya Juma'a a yankin Gaza.

Antonio Guteres ya bayyana matukar takaicinsa dangane da abin da ya faru, ya kuma bukaci kwamitin tsaro da ya gudanar da sahihin bincike kan hakikanin abin da ya faru.

A nata bangaren kasar Rasha ta dora alhakin abin da ya faru kaco kan kan irin salon siyasar zalinci ta Isra'ila akan Palastinawa.

Shi kuwa a nasa bangaren ministan harkokin wajen Iran Muhammad Jawad zarif, bayan yin Allah wadai da kakakusar murya kan kisan gillar da Isra'ila ta yi a kan palastinawa a jiya a Juma'a a yankin Gaza, ya kuma bayyana hakan a matsayin abin da yake tunawa duniya irin zaluncin da aka yi annabi Musa da jama'a raunana da suke tare da shi.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky