Amurka : Trump Ya Ce Zai Kakabawa Iran Wasu Takunkumai

Amurka : Trump Ya Ce Zai Kakabawa Iran Wasu Takunkumai

Shugaba Donald Trump na Amurka ya ce yana tunanin kakabawa Iran wasu sabbin jerin takunkumi kan shirin makamanta masu linzami da ma ayyukan a yankin gabas ta tsakiya.

Wannan dai ya biyo bayan da Mista Trump ya ce zai yi aiki da yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma a lokacin tsohon shugaban kasar Barack Obama.

A ranar 14 ga watan Yili na shekara 2015 ne mayan kasashen duniya da suka hada da Amurkar, Rasha Burtaniya, China, faransa da kuma Jamus suka cimma yarjejeniyar da kasar ta Iran kan shirin nukiliyarta na zamen lafiya da aka jiam ana takkadama akansa , sai dai tun lokacin Amurkar ta ki sakewa Iran din mara ta yadda zata mori yarjejeniyar.

Amurka dai na son Iran ta daina shirin makamanta masu linzami wanda kumadaina hakan  baya daga cikin yarjejniyar da aka cimma da ita.

Iran dai ta ce batun ta daina shirinta na makamai masu linzami batu ne da ko da wasa ba zata taba lamunta da shi ba, sannan kuma danganta rundunar kare juyin juya halin musulinci ta kasar da kuma kakaba mata wasu takunkumi a wannan bangarorin babbar barazana ce ga Amurka da sansaninta da ma dakarunta a yankin a cewar babban hafsan hafsoshin rundunar sojin Iran (IRGC) Janar Mohammad Baqeri.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky